What's Hot

Gwamnatin Kano ta karyata zargin karkatar da Naira biliyan 6.5

Table of Content

Gwamnatin Kano ta karyata zargin karkatar da Naira biliyan 6.5

A ‘yan kwanakin nan, kafafen sada zumunta na zamani sun cika da labaran ƙarya da zargi marasa tushe kan gaskiya, amana da nagartar wasu manyan jami’an siyasa na Gwamnatin Kano.

Ɗaya daga cikin irin wadannan labaran ƙarya da ake ganin an kitsa shi da gangan shi ne na jaridar Daily Nigerian, wata kafar labarai ta yanar gizo mai hedikwata a Kano,.

Jaridar ta wallafa wani labari a ranar 22 ga Agusta, 2025, inda ta zargi cewa an fitar da kuɗi daga baitul-mali na jihar Kano har naira biliyan 6.5 tare da karkatar da su.

Wannan zargi da ake yi, wanda a yanzu yana gaban kotu, akwai sunan Darakta Janar na Sashen Kula da al’amuran ofishin gwamna (Protocol Directorate) na Fadar Gwamnatin Kano, Alhaji Abdullahi Rogo.

Kan wannan ne ya sanya gwamnatin Kano ta magantu, inda ta bayyana matsayarta kamar haka.

  1. Ba tare da an tsoma baki cikin shari’ar da ke gaban kotu ba, gwamnati na ganin wajibi ta fayyace wa jama’a yadda Sashen Kula da Bako ke gudanar da aikinsa a Fadar Gwamnatin Kano, wanda bai bambanta da tsarin da ake bi a sauran jihohi da kuma gwamnatin tarayya ba.
  2. Da farko, gwamnati na jaddada cewa kowanne fitar kuɗi daga baitul-mali zuwa ga ma’aikatu, hukumomi da sassa na gwamnati (MDAs) ana yi ne bisa kasafi da aka tsara tare da lambobin lissafi da aka fayyace a tsarin kudi na shekara.

Saboda haka, babu wani mutum guda a cikin gwamnati da ke da ikon rike kuɗaɗen jama’a ba tare da takamaiman dalili da aka ware masa ba.

  1. Sashen protocols na Fadar Gwamnatin Kano na da manyan ayyuka da suka haɗa da jigilar baki, masauki, walwala, da kuma tsara tafiyar Gwamna a cikin gida da wajen ƙasar nan.
  2. Haka kuma, wannan sashi ne ke da alhakin samar da kayan aiki da bukatun jigila ga baki masu daraja kamar Shugaban Ƙasa, Ministoci, jami’an kasashen waje, da sauran baki na diflomasiyya da ke zuwa Kano a hukumance.

Wannan ya haɗa har da ‘yan ƙasa na gari da Gwamna ke bai wa kulawa ta musamman.

  1. Kusan kashi 95% na aikin wannan sashi ya ta’allaka ne da harkokin kuɗi masu yawa, wanda galibi ake biya ne a madadin jihar bisa umurnin Mai Girma Gwamna.
  2. Duk da haka, gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta ci gaba da zama mai kishin gaskiya, ingantacciyar tafiyar da kudi, bayyana gaskiya, da rashin yarda da cin hanci da rashawa, ba tare da ta yarda mutuncin jami’anta ya zube a hannun makirci na siyasa daga wasu marasa kishin kasa ba.
  3. Gwamnati na nanata cewa ba ta da wata shakka a kan gaskiya da amincin Darakta Janar na Sashen Kula da Baki Hon. Abdullahi Ibrahim Rogo.
  4. Muhimmin abu, gwamnatin NNPP za ta ci gaba da bude kofa ga suka bisa gaskiya da doka, amma ba za ta lamunci makircin siyasa ta hanyar yada ƙarya don bata sunan gwamnati ba.
  5. Gwamnatin Kano na sane da ayyukan wani bangaren adawa da ke ƙoƙarin tarwatsa mulkin yanzu ta hanyar yada irin waɗannan labarai a kafafen sada zumunta don yaudaran jama’a.
  6. A lokacin tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje, wannan sashin ne ya kashe sama da Naira biliyan 20 a cikin watanni uku kacal tsakanin Fabrairu zuwa Mayu 2023 bayan APC ta sha mummunan kaye a hannun NNPP.
  7. Tsawon shekaru takwas na mulkin da ta gabata, an yi fama da cin hanci da rashawa tare da asusun ɓoye-ɓoye na tsohuwar Uwar Gida da kuma sayen gidaje a Dubai da Saudiyya.
  8. Jama’ar Kano ba su manta da bidiyon cin hanci na daloli da ya shafi tsohon Gwamna Ganduje ba.
  9. A lokacin gwamnatin da ta gabata, kwace ƙasa da dukiyar jama’a ya zama ruwan dare ga iyalan masu daraja ta farko da mukarrabansu.
  10. Gwamnati na sane cewa jam’iyyar adawa ta buɗe ofishi musamman don rubuta ƙorafe-ƙorafe da nufin bata jami’an gwamnati mai ci yanzu da hana su tallafa wa Gwamna wajen gina Kano mai albarka.
  11. A cikin shekaru biyu da suka gabata na wannan gwamnati, masu zuba jari daga ciki da wajen ƙasar nan sun fara nuna sha’awa sosai a Kano saboda gaskiya da rikon amana.
  12. Jama’ar Kano da ma al’ummar Najeriya na yabawa gwamnatin Kwankwasiyya-Gida-Gida saboda gaskiya cikin tafiyar da gwamnati, wanda ya sa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya zama daya daga cikin gwamnonin da suka fi samun yabo a tarihin Mulkin jamhuriyyar Dimokradiyya ta hudu.
  13. Wannan ya tabbata ne ta hanyar lambobin yabo da dama da ake ta ba shi daga gida da waje.
  14. Gwamnati za ta ci gaba da girmama kafafen watsa labarai, amma ga waɗanda ke aiki bisa gaskiya da ka’idojin aikin jarida, ba waɗanda ke bari a yi amfani da su wajen yaudarar jama’a da ƙarya ba.
  15. Domin fayyacewa, Sashen Kula da Baki a kowace gwamnati aiki ne na gudanarwa kawai. Abinda aka dora masa shi ne tsara tarukan gwamnati, karɓar baki, shirya bukukuwa da jigila, da kuma kula da wasu buƙatu na musamman. Ba ya da ikon kashe kuɗi kai tsaye sai bisa tsarin gwamnati da amincewa bisa tsarin kasafi.
  16. Saboda haka, zargin da ake yadawa ba komai ba ne illa tatsuniya da aka tsara da gangan don siyasa da neman tasiri a zaben 2027.
  17. Jama’a su sani cewa gwamnatin Kano ba ta da abin boyewa . Kowanne jami’in gwamnati, ciki har da Darakta Janar na Protocol, na shirye ya bada cikakken bayani ga hukumomin yaƙi da cin hanci idan bukatar hakan ta taso.
  18. Don haka, jama’ar Kano su fahimci wannan makirci a matsayin shiri na adawa don bata gwamnati da dakile shirye-shiryen raya jihar. Amma wannan ƙarya ba za ta yi nasara ba
  19. Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kuduri aniyar ci gaba da tafiyar da gwamnati cikin gaskiya da adalci, kuma ba za ta lamunci ƙaryar siyasa ko propaganda su rushe wannan himma ba.
  20. Wannan gwamnati ta Kano ta gargadi masu adawa da su daina yada ƙarya, in ba haka ba za ta ɗauki matakan shari’a a kansu.
  21. Domin shari’ar tana gaban kotu mai hurumin sauraron irin wannan al’amari, gwamnatin Kano za ta bar kotu ta yi aikinta har sai lokacin da shari’ar ta kammala.

Sa hannu:
Sanusi Bature DawakinTofa
Darakta Janar,
Sashin Yaɗa Labarai da Huldar Jama’a
ba Fadar Gwamnatin Kano

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Kano CSO Leaders Distance Themselves from Coalition’s Corruption Allegation

‎Two prominent civil society leaders in Kano have publicly dissociated themselves from a recent statement credited to a coalition of Civil Society Organisations (CSOs) that demanded the suspension and prosecution of top state government officials over alleged corruption running into billions of naira.‎‎The coalition, which claimed to have over 20 signatories, had on Sunday called...

Kano State Ministry of Culture and Tourism Signs MoU with SparkLab Hub to Promote Culture and Tourism

In a major step toward promoting Kano State’s cultural heritage and boosting tourism, the Ministry of Culture and Tourism has signed a Memorandum of Understanding (MoU) with SparkLab Hub. The MoU is aimed at strengthening collaboration in key areas such as cultural preservation, promotion of historical sites, youth engagement, and leveraging technology for tourism development...

AKY Go Again Movement Appreciates Massive Turnout in Welcoming His Excellency Governor Abba Kabir Yusuf

The AKY Go Again Movement expresses profound appreciation to the people of Kano State, political and non-political organizations, and government officials who answered our call and came out in their thousands to welcome His Excellency, the Executive Governor of Kano State, Alhaji Abba Kabir Yusuf, on his return from the holy pilgrimage of Hajj. The...

Where Kano’s Story Unfolds”

Inside Kano is your premier online news platform dedicated to bringing you the latest happenings from across Kano. We provide timely, reliable, and engaging stories that cover everything from local events and politics to culture, business, and community updates.

Popular Categories

Must Read

©2025- All Right Reserved. Designed and Developed by Sparklab Creativity & Innovation Hub